Matatar Dangote za ta samar da lita man fetur miliyan 25 a kowace rana – NMDRA

Date:

 

Hukumar da ke sanya idanu kan harkokin man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta sanar da cewa sabuwar matatar mai ta Dangote za ta fara samar da lita miliyan 25 na man fetur a kowace rana ga kasuwannin Najeriya a cikin watan Satumbar da muke ciki.

Ana sa ran adadin man zai ƙaru zuwa lita miliyan 30 a kowace rana daga watan Oktoba.

Farashin Man Fetur ya yi tashin gwauron zabi a Nigeriya

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin sada zumuntarta na X ta bayyana cewa, a wani taro da suka yi a Abuja ranar Talata, NMDPRA da Kamfanin NNPCL sun amince da fara sayar da ɗanyen mai ga matatar Dangote da kuɗin ƙasar wato Naira.

Bayan shafe sama da shekara guda da taƙaddamar da aikinta a watan Mayun 2023, matatar Dangote, a ranar Talata, ta fara fitar da man fetur ɗin.

A jiya ne dai kamfanin NNPCL ta ƙara farashin man fetur daga naira 617 zuwa naira 897.

Aliko Dangote ya ce da zarar kamfaninsa ya kammala shirye-shirye da NNPCL, man fetur na kamfanin zai shiga kasuwa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...