Rahotanni da ke zuwa yanzu-yanzu daga titin Kaduna zuwa Abuja na cewa an samu cinkoson ababen hawa wanda ya tsayar da hanyar cak, inda ya sanya matafiya su ka yi cirko-cirko.
Wakilin Kadaura24 da ke kan titiin a halin yanzu ya rawaito cewa, wasu matafiya sun baiyana cewa cinkoson ababen hawan ya faru ne sakamakon faduwar wata babbar mota a dai-dai garin Katari, jihar Kaduna.
![Talla](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2024/08/IMG-20240821-WA0004-211x300.jpg)
Wani matafiye ya shaidawa Kadaura24 cewa lamarin ya faru ne tun jiya, lamarin da ya sa ake bin hannu daya,wanda ita ma daga bisa hanyar ta daina biyuwa.
An hangi fasinjoji da masu ababen hawa sun yi cirko-cirko a yayin da hanyar ta tsaya cak ba motsi.
Matafiyan dai, na fatan hukumomin lura da hanyoyi za su kai daukin gaggawa.
Hanyar dai ita ce babbar hanya da matafiya da suka fito daga Kano da Kaduna, Katsina da sauran su ke bi wajen zuwa babban birnin tarayya Abuja da kuma kudancin Nijeriya.