Daga Abubakar Sa’eed Suleman
Shahararren Dan wasan Bakwancin nan Alhaji Mato Yakubu Wanda akafi Sani da Malam Na-ta’ala a Cikin Shirin Dadin Kowa na Tashar Arewa24 yace Yana Jim Dadin yadda matarsa a Shirin Azumi take tausaya Masa.
Malam Na-ta’ala ya bayyana hakan ne yayin Wata ganawa da BBC Hausa sukai da shi a Cikin wani shirinsu Mai Suna “Daga Bakin Mai ita “.
Malam Na-ta’ala yace idan Azumi tana tausaya Masa a Cikin wasan sai yace gani Kamar matarsa ta gida ce ,a don hakan yace yana sha’awar ya Aureta a gaske.
“Idan da so samu ne a Cikin Matan da nake firm dasu akwai Matar da nake Bukata burina ya Cika na samu na Aureta , Saboda yadda take tausayi na a fim din sai nake ji tamkar matata ce ta gida , Wannan Mata kuwa itace Azumi”. Inji Malam Na-ta’ala Mai Shittin 10
Da aka tambaye shi akan Daya Matar tasa a Cikin Shirin wato Adam yace Bazai iya da itaba , inda yace ko a Shirin na Dadin Kowa ta isheshi.
Malam Na-ta’ala Wanda yace Yana da mata guda 3 Amma da Azumi zata amince da bukatar sa to da ya rufe Kofa da ita.
Really interesting👍Allah ya ida nufi.🤲
Idan har yay hakan wlh yayi daidai Kuma yataimakamata itama dataringa fitowa afilm ai gara aganta a dakin mijinta Dan duk wani daraja na mace shine mijin auranta by ummah labaran Muhammad gwammaja 0806842996 Mai waqar siffaturrasul S A W