Shugaban ƙasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu zai bar kasar zuwa kasar faransa a ranar litinin 19 ga watan Ugusta, 2024.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Zargin Sayo Magani: Jam&’iyyar APC ta yi wa gwamnatin Kano raddi kan rahoton Dan Bello
Sai dai sanarwar ta ba bayyana takamaiman ranar da shugaban kasa zai dawo Nigeria ba.
” Shugaba Tinubu zai dawo Nigeria bayan ya kammala ‘yar gajeriyar ziyarar aiki da ya kai kasar ta faransa.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a makon da ya ke karewa Shugaba Tinubu ya ziyarci kasar Equatorial Genie domin sanya hannu kan wata yarjejeniya.