Dalilin da ya sa na fara yiwa yan siyasa bankada – Dan Bello

Date:

 

 

 

Dr.Bello Habib Galadanchi, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, mai barkwanci a shafukan sada zumunta, ya ce ’yan siyasar Najeriya suna azabtar da yan ƙasar ta hanyar wawure kudin kasar.

“Yan Nigeria na fama da yunwa sakamakon manufofin tattalin arziƙin Shugaba Bola Tinubu ya ɓullo da su”.

Ɗan Bello ya bayyana hakan ne, yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Daily Politics na gidan talabijin na Trust TV a ranar Talata.

Ya ƙalubalanci gwamnati mai ci, cewa su kai shi kara idan ba sa jin daɗin abin da yake yi.

Tinubu na iya bakin kokarinsa don gyara Nigeria – Minista A T Gwarzo

Ya jaddada cewa ba shi da wata alaƙa da kowace jam’iyyar siyasa a Najeriya, kuma ba ya yi wa kowa aiki.

Bello ya ce, “Idan abin da nake yi ya dame su, hakan yana nufin yana taimaka wa mutane. Idan manufofinsu suna da kyau, mutane ba za su ji cewa abin da nake yi yana kawo sauyi ba. Amma abin da yake faruwa yana nuna cewa abubuwan da suke yi na haifar da matsaloli.

“Manufofin gwamnati suna sa mutane cikin yunwa. Mutane na mutuwa. Wasu ma suna cin ciyawa suna sha ruwan da ya lalace. Wasu suna zuwa gida-gida suna neman a ba su ci abincin da za su ci.

Abubunwan da aka tattauna tsakanin Tinubu Buhari Jonathan da gwamnonin Nigeria

“Wannan ba annoba ba ce; manufofi ne da za a iya kauce musu. Shugabannin sun samar da waɗannan manufofi sannan suka yi kunnen uwar-shegu da abin da suka haifar.

“Yanzu suna fushi saboda muna magana kan waɗannan manufofi. Suna son mu yi shiru yayinbda mutane ke fama da wahala. Da gaske? Ina mutuncinmu yake? Me ya sa za mu yi shiru yayin da muka san cewar yadda abubuwa ke tafiya a sauran ƙasashe, inda mutane ba sa fama da yunwa?

“Suna fushi saboda suna tara biliyoyin Naira suna yin ayyukan shirme. Eh, ina son su ji haushi. Ina son su kai ni kotu, su yi duk abin da za su iya domin su sa mu yi shiru. Wannan yana nufin cewa aikinmu yana ƙara yin tasiri.”

Matashin mai barkwanci, ya kan yi amfani da kafofin sada zumunta wajen aike da saƙo cikin shaguɓe ga ‘yan siyasa da sauran al’umma.

Sai dai a ’yan kwanakin nan sunansa ya karaɗe kafafen sada zumunta, sakamakon wani bidiyon zargin badaƙalar kuɗaɗe da ya sa ki game da tsohon mataimakin ɗan gwamnan Kano a jami’yyar APC, Murtala Sule Garo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...