Daga Rukayya Abdullahi Maida
Karamin ministan gidaje da raya birane na Nigeria Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yana bakin kokarinsa wajen gyara matsalolin kasar.
Ministan ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar APC 4G Forum na Kano da suka kai masa ziyarar ban girma a ofishin sa.
Ya bayyana cewa a halin yanzu shugaban kasar ya kaddamar da ayyuka da dama wadanda aka samar da su da niyya magance matsalolin da ke addabar al’umma.
Abubunwan da aka tattauna tsakanin Tinubu Buhari Jonathan da gwamnonin Nigeria
Minista Gwarzo ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar APC 4G Forum na Kano da su tabbatar da hadin kan jam’iyyar tare da bayar da gagarumar gudunmuwa don samun nasarar Shugaba Bola Ahmad Tinubu a yunkurinsa na sake dawo da kasar nan kan saiti.
Ya kuma shawarci kungiyar da ta hada kan dukkan ‘ya’yan jam’iyyar karkashin inuwa daya domin gujewa maimaita kurakuran da aka yi a baya. Ya kara da cewa ya kamata kowa ya tashi tsaye domin tallata gwamnatin Bola Tinubu.
Tun da farko, Shugaban rikon kungiyar APC 4G Forum na Kano, Kwamared Sale Jeli (Sarkin Fadar Karaye) ya bayyana nagartar Ministan, inda ya bayyana shi a matsayin jagora na gari mai kishin kasa, wanda a kodayaushe ya ba da fifiko wajen yi wa al’ummarsa hidima.
Da dumi-dumi: Tinubu zai tafi ƙasar Equatorial Guinea
A sanawar da mai magana da yawun Ministan Adamu Abdullahi ya aikowa kadaura24, ya ce Kwamared Jeli ya yabawa Ministan bisa kawo aikin rukunin gidaje guda 500 a Kano wanda a cewar sa ba a taba yin irinsa ba a jihar.
Ya kuma ba da tabbacin kungiyar a shirye ta ke wajen bayar da goyon baya da hadin kai domin samun nasarar gwamnatin shugaban kasa.