Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya cire dokar hana zirga-zirga da aka kakaba a biranen Kaduna da Zariya.
Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya sanar cewa umarnin cire dokar hana fita a Kaduna da Zariya ta fara aiki nan take.
Yadda aka sace Naira biliyan 50 daga asusun Gwamnatin Kano
Idan za a tunawa a makon da ya gabata ne gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita sakamakon yadda wasu bata gari suka fake da Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa suka rika fashe-fashen da sace kayan gwamnati dana al’umma.