Daga Rahama Umar Kwaru
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Salman-Dogo Garba, ya ce rundunar ba ta da labarin asarar rai a lokacin zanga-zangar yunwa da tsadar rayuwa da aka gudanar.
Kwamishinan ya bayyana haka ne ranar Litinin a lokacin ganawarsa da ’yan jarida, inda ya ce rundunar ta kama mutane 873 kan laifin lalatawa da sace dukiyoyin jama’a da na gwamnati a lokacin zanga-zangar.
“A iya bayanan da muke da su, zuwa yanzu ba mu da rahoton asarar rai a yayin zanga-zangar,” in ji shi.
Dan Bello ya sanya wa jam’iyyar APCn Kano sharadin dakatar da yi mata bankade-bankade
Idan za a iya tunawa Daily trust ta kawo rahoton iyalan wasu matasa akalla uku da aka kashe a lokacin zanga-zangar, ciki har da wata budurwa da ake shirin daura aurenta.
Yan uwan wadanda aka kashe din, sun kuma yi zargin yan uwannasu sun rasu ne a sakamkon harbi daga jami’an tsaro, musamman ’yan sanda.
Iyalan wadanda suka rasun dai sun bayyana damuwa bisa yadda zanga-zangar da aka shirya ta lumana ta yi ajalinsu, inda suka bukaci a bi musu hakkinsu.
Zanga-zangar lumanar ta rikide zuwa tarzoma ne bayan da bata-gari suka kwace ta, suka rika fasa wurare suna sace-sace, tare da jikkata mutane a sassan jihar.
Yadda aka sace Naira biliyan 50 daga asusun Gwamnatin Kano
An yi dauki ba dadi tsakanin bata-garin da jami’an tsaro a kofar gidan gwamnatin jihar da sauran sassan jihar, inda aka kama sama da mutum 100.
Kazancewar lamarin ya kai ga gwamnatinn jihar, Abba Kabir, sanya dokar hana fita tsawon awa 24, kafin daga bisani a sassauta dokar.
Daily trust