Daruruwan masu zanga-zangar ne suka mamaye titunan Kano a ranar lahadi, a ci gaba da zanga-zangar adawa da yunwa da rashin shugabanci nagari a fadin Nigeria.
Zanga-zangar dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya yiwa yan ƙasar jawabi, inda ya shaida wa matasan cewa ya ji su da babbar murya don haka a dakatar da zanga-zangar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 zuwa sa’o’i shida (8 na safe zuwa 2 na rana) domin saukaka al’umma jihar .
Zanga-zangar dai galibi matasa ne aka ce sun gudanar da ita a kewayen unguwannin Bakin Zuwo da Koki a karamar hukumar Dala da Sharada a karamar hukumar birni da Gadon Kaya a karamar hukumar Gwale sai kuma bridge a karamar hukumar Nasarawa.
Atiku ya yi Allah-wadai da harbin masu zanga-zanga a Kano, Abuja, ya kai karar Tinubu UN da ICC
Kadaura24 ta rawaito an gano masu zanga-zanga dauke da tutar ƙasar Rasha suna cewa suna neman shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya kawo musu dauk.
Wani ganau a garin Bakin Zuwo, Malam Salisu ya ce masu zanga-zangar na dawa a kan titi, sun fito domin nuna adawa da rashin shugabanci nagari a Nigeria.
“Na ga masu zanga-zangar suna da yawa, sun fito kamar da misalin karfe 10 na safe, suna rike da tutar Rasha. Suna yin zanga-zangar ne don nuna rashin amincewarsu da matsalolin rashin tsaro da wahalar rayuwa da sauransu,” in ji Salisu.
Rundunar yan sanda ta Kano ta yi karin haske kan abun da ya faru a unguwar kurna
Sai dai a yankin unguwar Fagge al’umma sun fito inda suka gudanar da Sallah da alkunutu domin neman sauke a wajen Allah Subhanahu wata’ala, Sannan daga bisani suka fara Zanga-zangar.
Haka kuma, wakilin kadaura24 ta gano yadda aka tsaurara tsaro a manyan Kasuwar jihar, kamar kantin kwari da sabon gari da Dawanau, Inda aka jibge Sojoji don ganin ba a sami wata matsala ba .