Daga Isa Ahmad Getso
Tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya gargadi jami’an tsaro kan musgunawa masu zanga-zanga.
Akwai rahotannin da ke cewa wasu matasan Najeriya da ke zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya sun shiga hannun ‘yan sanda da wasu jami’an tsaro.

An yi zargin an harbe wasu masu zanga-zangar ranar Asabar a jihar Kano bayan zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta rikide zuwa tashin hankali.
Da yake magana kan lamarin, Dino Melaye a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X wato Twitter, ya bayyana rashin gamsuwa da yadda jami’an tsaro su ke cin zarafin masu zanga-zangar.
Rundunar yan sanda ta Kano ta yi karin haske kan abun da ya faru a unguwar kurna
Ya kuma bukaci jami’an da su daina cin zarafin masu zanga-zangar, domin tabarbarewar tattalin arzikin ya shafar kowa da kowa ciki har da su.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kasuwa daya muke zuwa da ku, gidan mai daya, Naira daya muke kashewa, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ba su da wata kasuwa ta musamman ko gidan mai na musamman.
“Ku kula da mutane da girmama su, domin yan uwanku ne idan zaukin ya zo kuma za ku amfana, kuma dokar kasa ce ta basu damar yin hakan ”.