Rundunar yan sanda ta Kano ta yi karin haske kan abun da ya faru a unguwar kurna

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar yan sandan jihar kano ta bayyana cewa al’ummar unguwar yankin unguwar kurna da rijiyar lemo ne suka fara afkawa Ofishin yan sanda na yankin a kokarinsu na kokarin dole sai sun cigaba da zanga-zanga duk da dokar hana fita da aka sanya.

” Mun sami labarin cewa wasu matasan unguwar Kurna da Rijiyar lemo suna kokarin afkawa jami’anmu, hakan tasa aka tura karin jami’an tsaro da ke kusa da yankin domin ganin matasan ba su yi nasara ba.

Talla
Talla

Kadaura24 ta rawaito Kakakin rundunar yan sandan jihar kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin shirin “Dan Sanda Abokin Kowa” na gidan radiyon Freedom dake Kano.

Amnesty ta Magantu Kan Kisan Masu Zanga-Zanga a Kano

SP Kiyawa ya ce yayi mamakin yadda ya gani a dandalin sada zumunta mutane suna ta yasa abun da ba haka nan yake ba, musamman kan lamarin da ya faru a unguwar kurna.

” Matasan suna so su sami galabar yan sanda ne ta hanyar kona chaji Ofis din yan dake yanki, domin su sami damar cin karensu babu babbaka, ta hanyar shiga shagunan mutane domin yi musu sata”. Inji Kiyawa

Ya ce yanzu haka suna cigaba da gudanar da bincike domin kara samun bayanai sosai don fitowa domin yi wa al’ummar jihar Kano cikakken bayani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...