Shugaban kasa Bola Tinubu na kallon yadda zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ke gudana a fadin Nigeria.
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin din channels .
Zanga-zangar da aka yi a Najeriya a baya-bayan nan na da nasaba da tsadar rayuwa, da tabarbarewar farashin Naira da kuma cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi.

Ko da yake an yi ta kiraye-kirayen ga Tinubu ya yi jawabi ga al’ummar kasar bayan zanga-zangar ta shiga kwana na uku, amma har yanzu shugaba Tinubu bai yi hakan ba.
Sai dai Bagudu, ya ce shugaban na Najeriya ya san halin da ake ciki sosai.
“Shugaban kasa ya na sane da halin da ake ciki, yadda ya kamata .”in ji Ministan
Yadda Jaruma Rahama Sadau ta raba Naira Miliyan 1 ga Masoyanta
”Ni minista ne. Akwai nauyi akai na. Ni ma ina bibiyar halin da ake ciki saboda na sami abun da zan ce game da bayanan da zan shigar.”
Bagudu ya ce “Mu na ji kuma mu na kallon abun da ke faruwa game da zanga-zangar.”
Dan Iliyasu Satame da al’ummar Obajana za su shiryawa Ɗangote saukar alqur’ani 10
Ministan wanda ya amince da cewa ana shan wahala a Najeriya, amma gwamnatin tarayya na kokarin ganin an samu saukin rayuwa ga ‘yan kasar.
“Duk duniya ana fuskantar matsalar tsadar rayuwa rayuwa, amma za mu saurara kuma muna kuma daraja abubuwan da ‘yan Najeriya ke fada”.
Solacebase