Yadda Jaruma Rahama Sadau ta raba Naira Miliyan 1 ga Masoyanta

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

Shahararriyar jarumar nan Rahama Sadau da ta yi fice a fina-finan duniya ta rabawa mabiya shafinta na Facebook zunzuruntun kudi har Naira Miliyan 1.

Jarumar dai ajiya ta wallafa cewa za ta raba kudi ga wasu mutane 100 wanda za ta zaba kai tsaye da kanta inda wasu har suna ganin lamarin wasa ne kwatsam sai akaji saukar dubu 10, 10 ga mutanen da suka aje lambar Asusun Bankinsu.

Talla
Talla

Sadau Yar Najeria ce Wadda ta Fara Fim Daga Masana’antar Kannywood har takai kololuwar mataki a fannin fina-finan Duniya Inda ba iya Najeria ba har kasashen ketare na Alfahari da ita.

Idan zanga-zanga ta ƙazance to fa za mu ɗau mataki — Sojoji

Wani abun ban sha’awa na Jarumar Shi ne Yadda Babu girman kai a tare da ita take iya bibiyar mabiyan nata ta yi musu like ko Comment wani Zubin Dama Sharing Abinda suka rubuta hakan yasa wata shakuwa tsakaninta da Mabiyanta a yanzu da sabuwar soyayya.

Rahama dai ta sake dawowa a fagen shuhura inda da dama suke alakanta girmama mutane da Ra’ayinta da Ilimin da take dashi bata duba daukaka, dubun dubatar mutane suna kara nuna soyayyarsu agareta inda har yanzu Soyayyar ke nuna cewa Acikin Mata Masu Fina Finai Babu Kamarta.

Mutanen da suka sami kyautar kudin sun bayyana Jin dadinsu, inda suke cewa Jarumar ta tallafa musu a daidai lokacin da suke bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...