Gwamnatin jihar Jigawa ta dage dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta saka sakamakon zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ta rikide zuwa tarzoma.
Kwamishinan yada labarai na jihar Jigawa Sagir Musa ne ya bayyana hakan a gidan gwamnati dake Dutse a ranar Asabar.

Ya ce matakin ya biyo bayan fahimtar cewa Abubuwa sun lafa, jihar ta Kasance cikin kwanciyar hankali a hali a yanzu.
Dan Iliyasu Satame da al’ummar Obajana za su shiryawa Ɗangote saukar alqur’ani 10
A halin da ake ciki kuma, rundunar ‘yan sandan ta kama sama da mutane 200 da ake zargi da wawure dukiyar jama’a tare da kwato kayayyakin da aka sace.
“Mutane da yawa ‘yan sanda sun kama su, inda jami’an tsaro suka kama mutane sama da 200 a jihar,” in ji shi.