Gwamnan jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahya ya baiyana Rasuwar Mahaifiyar Sarakunan Kano da Bichi Hajiya Maryam Ado Bayero da cewa Babban rashi ne ba ga jihar Kano Kadai ba har da Kasa baki Daya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin daya jagoranci Wata Babbar Tawaga daga jihar Gombe zuwa Kano dokin yin ta’aziyyar rasuwar Mai Babban Daki ga Gwamnatin jihar Kano da al’ummar Kano Baki Daya.
Alhaji Inuwa Yahya yace Akwai dadaddiyar alaka tsakanin jihar Kano da jihar Gombe tun Shekara daruruwa da Suka gaba, yace hakance tasa ya Jago tawagarin domin yiwa al’ummar jihar Kano ta’aziyya na Babban rashi da sukayi.
Gwamnan yayi addu’ar samun Rahamar Allah madaukakin Sarki ga Mai Babban Daki da sauran al’ummar musulmi Baki daya .
A Jawabinsa Gwamnan jihar Kano ya yabawa takwaran nasa na Gombe da Al’ummar jihar Gombe bisa Wannan ziyarar da suka Kawo Jihar Kano domin yin ta’aziyyar rasuwar Mai Babban Daki.
Tawagar Gwamnan jihar Gombe akwai Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar IIi da sauran Masu ruwa da tsaki a Jihar Gombe.