Daga Sani Magaji Garko
Gwamnatin jihar Kano ta gargadi manoma da su guji yin amfani da kayayyakin da suka lalace Wanda kamfanoni ke fitarwa a matsayin taki.
Cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hanun jami’in hulda da jamaa na maaikatar Muhalli ta jihar Kano Sanusi Abdullahi Kofar Na’isa ya fitar ta ambato kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso na bayyana hakan lokacin taron masu ruwa da tsaki na maaikatar Muhalli ta jihar Kano.
Kwamishinan ya ce yin amfani da kayayyakin da suka lalace ko aka fitar da su day kamfanoni a matsayin taki ga tsirrai ka iya haifar da matsalar ciwon Koda da duk Wanda yake cin ire-iren wadannan kayayyakin amfanin gona a ko da yaushe.
Ya ce iya matsala kawai ire-iren wadannan kayayyakin ke da shi kawai ba, domin ba su day sinadaran da ‘yan’yan itatuwar ke bukata domin girma ko kuma domin samar da yabanya.
Dakta Kabiru Getso ya ce yawancin guraren da sukafi samun irin wannan matsalar sun hada da Wudil da Gezawa da Tamburawa da Dawakin Kudu da sauran su.
Daga nan yayi Kira ga alummar da suke zaune a guraren da suke da kamfanoni musamman Sharada da Chalawa da su guji yin amfani da lalatattun kayayyakin da kamfanoni ki zubarwa.
Kwamishinan ya ce Nan gaba kadan maaikatar Muhalli zata fara gangamin wayar da kan al’umma game da matsalar.