Daga Samira Ahmad
Shugabar riko ta karamar hukumar wudil Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ta ce zata hada gwiwa da hukumar masu yiwa kasa hidima wajen ba da magunguna kyauta da al’ummar karamar hukumar.
“Cikin wata yarjejeniyar haɗin gwuiwa da mukayi tsakanin Ƙaramar Hukumar Wudil da reshen ɗalibai masu bautawa ƙasa (NYSC) na Wudil, zamu gudanar da wata shirin dubawa da rabon magungunnan cututtuka irin su hawan jini, zazzaɓin typhoid da shauran nau’ikan gama garin cututtuka”.
Hajiya Bilkisu Indabo ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa da jaridar kadaura24.
“In sha Allahu nan da ƴan kwanaki kaɗan zamu sanar da ranar da zamu gudanar da wannan taro domin al’ummar Ƙaramar Hukumar Wudil su fito su amfana”. Inji Shugabar
Rarara ya Magantu AKan Goge Shafinsa da Facebook Ya Yi
Ta ce da ma bannin kula da lafiyar al’umma na daga cikin manyan abubunwan da ta fi baiwa muhimmanci, ta kuma yi alkawarin cigaba da Kula da lafiya da Ilimi a karamar hukumar .
“Kamar yadda aka sani, a matsayi na ta ma’aikaciyar lafiya kuma malamar ilimi, zan cigaba da bayarda da fifiko a wannan ɓangare dama shauran ɓangarori masu amfani kai tsaye ga al’umma ta domin bauta musu yadda ya dace”. A cewar Bilkisu Indabo