Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
A halin yanzu dai shugaban ƙasa Bola Tinubu, yana ganawa da gwamnonin jam’iyyar APC da wasu a a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.
Duk da cewa ba a bayyana dalilin taron ga manema labarai ba wanda suke gudanar da shi yau Alhamis, a fadar gwamnati amma ana kyautata zaton yana da nasaba da shirin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka shirya gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta, 2024.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma ne, ya jagoranci tawagar gwamnonin zuwa fadar shugaban kasa tare da shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), kuma Gwamna jihar Kwara, AbdulRazaq AbdulRahman.
Kotun ta yanke hukunci ga wanda ya tsakawa jami’in NDLEA wuka a Kano
Haka kuma an ga mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu, da Gwamnan jihar Benue, Hycinth Alia da takwarorinsa Uba Sani na jihar Kaduna da na jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, da dai sauransu duk a fadar shugaban ƙasa.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hadar da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribado da Ministan Kudi Wale Edun da Atiku Bagudu ministan kasafi da tsare-tsare da dai sauransu.