A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da sarakunan gargajiya a fadar Aso Rock Villa dake Abuja.
Wadanda suka jagoranci tawagar sarakunan sun hada da Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.
An fara taron ne da misalin karfe 2:30 na rana lokacin da shugaban ya isa zauren majalisar.
Sojoji Sun Gargaɗi Masu Shirin Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa
Ko da yake ba a san jadawalin taron na ranar Alhamis ba, amma ana ganin yana da alaƙa da kiraye-kirayen yin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ake ciki a fadin kasar, wanda aka shirya yi a ranar 1 – 10 ga Agusta, 2024.

Zanga-zangar, wacce aka yi mata take da ‘EndBadGovernance,’ ta sami karbuwa sosai a shafukan sada zumunta, har yanxu ba a sanan wadanda suka shirya zanga-zangar ba.
A wajen taron akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da babban sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun.

Akwai kuma Gwamna Abdulrazaq Abdulrahman na jihar Kwara, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, da Hope Uzodinma na jihar Imo, wanda ke jagorantar kungiyar gwamnonin APC.
Sai Ministan Kudi Wale Edun, da Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu.