Wata Babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta dakatar da Alhaji Aminu Ado Bayero da wasu sarakuna hudu da aka tsige daga karagar mulki daga cigaba da bayyana kawunansu a matsayin sarakunan Kano, Bichi, Rano, Gaya, Karaye.
Justice watch ta rawaito da take zartar da hukuncin a yau, kotun ta kara jaddada cewa sarkin Kano na 15 da wasu sarakuna hudu da duk wanda suka nada daga cigaba da bayyana kansu a matsayin sarakunan Kano, Bichi, Gaya, Rano, Karaye da kuma hakimai da sauransu.
Cikakkun bayani na nan tafe