Bani da zabin da ya wuce tallafawa al’ummar da suka zabeni – Kabiru Dan-Hassan

Date:

Daga Sufyan Dantala Jobawa
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kura, madobi da Garun mallam, Kabiru Idris Dan-Hassan ya bukaci shugabanni da ma gwamnatoci da su samar da tsarin tallafawa al’umma a wannan lokaci da aka shiga matsin rayuwa da tsadar kayayyaki.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke mika na’urorin rarraba hasken wutar -lantarki wato(Transformers) da kuma na’urorin samar da hasken wutar lantarki masu aiki da hasken rana ga al’ummomin da ya ke wakilta.
Yace la’akari da yanayin da ake ciki ya zamarwa Shugabani dole su Shigo Cikin al’ummar su domin tallafa musu su fita daga Cikin mawuyacin halin da ake ciki.
Kabiru Idris Dan-Hassan wanda Bello Datti Kura, ya wakilce ya bukaci mawadata da su rinka tallafawa masu karamin karfi a tsakanin al’umma domin rage musu radadin talauci da ake fama dashi.
Daga bisani Dan Majalisar ya kuma ba da tabbacin tallafawa bangaren lafiya da sauran fannonin cigaban rayuwar al’umma, inda ya ce yana baiwa aiyukan raya kasa fifiko da nufin cigaban mutanen da ya ke wakilta.
Shi ko a nasa bangaren, shugaban karamar hukumar Garun mallam Mudansur Aliyu Dakasoye wanda ya yi jawabi a madadin sauran takwarorinsa sun bada tabbacin wayar da kan al’umma domin kulawa da kayayyakin da aka samar musu don inganta rayuwar su.
Daga cikin wuraren da suka amfana sun hadar da kofar yamma a garin Kura da Garin Yanaba dake karamar hukumar Garun mallam, sai kuma cikin garin madobi a karamar hukumar madobi.

1 COMMENT

  1. Agaskiya hakane afada achika Sai Dan kunya transformer tazo yanaba Dan àllah katai maka a janyo way zuwa tsaure nagode daga surajo tsaure

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...