Bayanan da ke fitowa daga majalisar dokokin jihar Kano na cewa a yau ne ‘yan majalisar za su kammala aiki a kan dokar da ta kafa sabbin masarautu a jihar.
Waɗansu majiyoyi masu ƙarfi sun tabbatar wa BBC cewa ‘yan majalisar za su soke dokar da aka yi a shekarar 2019, wadda ta bayar da damar kafa ƙarin manyan masarautu huɗu a cikin jihar.
Abun da ya faru a majalisar dokokin jihar kano kan batun gyaran dokar masarautu
Dokar ta ƙirkiri masarautar Bichi da ta Karaye da ta Gaya da kuma masarautar Rano.Tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanya hannu a dokar a watan Disambar 2019.
A halin yanzu dai an girke jami‘an tsaro a wurare da dama na birnin Kano domin kauce wa tashin hankali.
Waɗansu majiyoyi a Kano ɗin sun tabbatar da cewa da zarar majalisar ta kammala kwaskwarima a kan dokar, ba tare da ɓata lokaci ba za ta mika wa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf .
Kuma ana sa ran gwamnan na Kano zai sanya hannu a kan dokar kafin sanar da rushe sabbin masarautun da aka kafa a shekara ta 2019.