Daga Ibrahim Aminu Riminkebe.
Babbar kotun shari’ar musulunci dake zaman ta a shahuci karkashin jgaorancin mai shari’a Malam Abdu Abdullahi Wayya, ta bada umarnin ayo sammacin ‘yar siyasar nan mai suna Sadiya Dauda Ican Kabari ta ko wacce ta hanya.
A zaman kotun na yau laraba, lauyan bangaran masu kara Barista Tanimu ya bayyana wa kotun cewa wacce ake zargin ta jima tana gujewa shari’a, duk da sammacin da kotun tayi umarnin a baiwa Sadiya Dauda Ican Kabari domin ta bayyana a gaban kotun.
Barista Tanimu ya shaidawa kotun cewa, wacce ake zargin ta yi wani fefan bidiyo Inda ta bata sunan mahaifi mai kara Adamu Abdullahi Karkasara wanda kuma ta watsa bidiyo a kafafan sada zumunta.
Abun da ya faru a majalisar dokokin jihar kano kan batun gyaran dokar masarautu
Hakazalika lauyan masu kara ya sake bayyanawa kotun cewa, mako guda kenan ana neman Sadiya Ican Kabari domin a bata sammacin amma tana kaucewa hakan saboda yadda ta rufe daukacin wayoyin da take amfani dasu.
Hajjin Bana: Ƙasar Saudiyya Ta Samar Da Wata Lema Ta Musamman Ga Mahajjata
Daga bisani mai shari’a Malam Abdu Abdullahi Wayya, ya amince da rokon bangaran masu kara suka yi, tare da yin umarnin sake aikewa Sadiya Dauda Ican Kabari sabon sammacin ta hanyar like mata shi a kofar gidan ta da sakon tartakwana da kuma hanyar Whatsapp domin ta bayyana a kotun.
Alkalin kotun ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar biyar ga watan gobe domin ci gaba da sauraron shari’ar.