Daga Hafsat Abdullahi
Shugaban kuma wanda ya kafa jami’ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University a Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayyana rasuwar shahararriyar mawakiyar Hausa nan, Hajiya Magajiya Danbatta a matsayin babban rashi ga daukacin al’ummar Arewacin Najeriya.
A cikin sakon ta’aziyyar da ke kunshe a cikin wata sanarwa da Shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya Sanyawa hannu daga Faransa wadda aka aikowa Kadaura24, ta bayyana rasuwar Magajiya Danbatta a matsayin mai Babban Rashi ga al’umma baki daya.
La’akari da Gudummawar da Marigayiyar ta baiwa al’umma ta hanyar fadakarwa ta Waka Hukuma Gudanarwar Jami’ar ta sanya wa ginin koya Koyar da harkokin Shari’a ta Jami’ar sunan Marigayi Tsohuwar mawakiyar Arewa, Hajiya Magajiya Danbatta baya ga karrama ta bayan rasuwarta.
“Don girmama Marigayi Magajiya Danbatta (Halima Malam Lasan) da gudunmawar da ta bayar a fannin ilimi, mun yanke shawarar karrama ta da digirin girmamawa bayan rasuwa.”
Sanarwar ta kara da cewa “mun yi shirin karrama ta a lokacin tana da rai amma, ta mutu kafin Lokacin taron.”
Wannan, sanarwar ta ce, baya ga sanyawa Sashen Shari’a suna. Marigayiyar sun ce “Za mu yi rashin barkwancinta da shahararrun waƙoƙinta”.
Farfesa Abubakar Gwarzo, wanda shi ne a matsayin Shugaban Kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu a Afirka ya bayyana rashin Magajiya Danbatta a matsayin abin takaici. Inda Sanarwar tace a madadin iyalansa da daukacin Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University, yana mika ta’aziyar su ga iyalai da abokan arzikin marigayiyar da ma daukacin al’ummar Jihar Kano da Najeriya baki daya.
Fitacciyar mawakiyar Hausa, Halima Malam Lasan, wacce aka fi sani da Magajiya Danbatta ta rasu tana da shekaru 85 bayan gajeruwar jinya a babban asibitin Danbatta a ranar Juma’a 8 ga Oktoba 2021.
Guda daga cikin waƙoƙin ta ta bada gudummawa sosai wajen sanya yara sama da 3,000 a makarantu a farkon Shekarar 1970.
Idan za a iya tunawa a shekarar da ta gabata, Gidauniyar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ta hada kai da wasu mutane don tara kudade don tallafawa Marigayiyar Mawakiyar wanda ya kai ga gina Gida da samar mata da kayan abinci.
Rahoton ya ce marigayiya Dambatta ta makance saboda mawuyacin halin rayuwa data shiga wanda ya kai ta ga yin bara.
Farfesa Gwarzo ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya baiwa Marigayiyar Aljannah Firdaus tare da baiwa iyalinta juriyar jure rashinta.
Веном 2 – смотреть онлайн в хорошем качестве https://bit.ly/venom2-2021
Веном 2 – смотреть онлайн в хорошем качестве https://bit.ly/venom2-2021