Bincike: Shin ko Kun San abun da yake jawo Nankarwa a jikin Mata?

Date:

Nankarwa wani yanayi ne da aka fi samunsa a jikin fatar mata, musamman masu ciki.

Hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS ta ce nankarwa ba ta cutarwa don ba ta janyo wata matsalar kiwon lafiya.

Alama ta farko da watakila mace za ta ji idan nankarwa za ta fito mata, ita ce za ta ji kaikayi a dai dai kan fatar da ta bude. Inji hukumar.

Haka zalika idan ta dade a jikin mace ta kan koma ta zama ba a ganinta sosai, ko kuma ta zama kamar tabo mai haske.

Kadan daga cikin dalilin da hukumar ta ce suna janyo nankarwa sun hada da, idan ke mace ce, ko idan kina amfani da mayukan shafe-shafe, ko wasu kwayoyin magani, ko kiba ko rama cikin kankanin lokaci.

Wuraren da ta fi fitowa a jiki, a cewar NHS sun hada da kan fatar ciki da cinya da damtse da kirji da kan mama da baya.

Haka zalika nankarwa ta kan zo da launuka daban-daban da suka hada da ruwan hoda ko ja ko ruwan goro ko baki da dai sauransu.

Sai dai bambancin launin ya danganta ne da launin fatar mace.

Haka kuma yadda ta ke fitowa ya danganta ne daga wannan mace zuwa wancan.

NHS ta kara da cewa masu ciki da dama na yin nankarwa, inda mai juna biyu kusan takwas a cikin goma ke fuskantar wannan yanayi.

Idan mace ta kara jiki fiye da kima a lokacin da take da ciki, akwai yiyuwar ta samu nankarwa.

Amma hakan kuma ya danganta da jikin mace kafin ta samu juna biyun.

Mata da dama dai na kara kilo 10 zuwa kilo 12 da rabi a lokacin da suke da ciki, a cewar hukumar, amma hakan ma dai ya bambanta a tsakanin mata.

Sai dai hukumar ta bayar da shawarar cewa yana da kyau mace ta ci abinci mai gina jiki a lokacin da take da ciki.

Amma ta jaddada cewa kada mai ciki ta ci abincin da ake hadawa don neman rage kiba.

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An sanya dokar hana fita a Jigawa

An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare...

Gwamnan Kano ya bayyana abun da gwamnatin za ta yi a filin Idi

  Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar...

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...