October 19, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Anyi taron zagayowar Ranar masu Amosani Kashi ta Duniya a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi

 

An bukaci al’umma su kasance masu ziyartar asibitoci domin bincikar lafiyarsu lokaci zuwa lokaci bawai sai sun kamu da rashin lafiya ba.

 

Wani gwararran likitan kashi dake aiki a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Dr musa bello kofar Na’isa ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar a dakin taro na kwalejin Zara na Nono dake dorayi babba a Kano.

 

Taron wanda kungiyar masu fama da larurar amosanin kashi ta arewa ta shirya a wani bangare na ga bikin tunawa da masu amosani kashi
Wanda Majalisar Dinkin duniya ta ware ranar 12 ga watan oktobar kowace shekara a Matsayin ranarsu ta Duniya .

 

Dr Musa yace Rashin zuwa asibitin domin duba Lafiyar Mutane Kan jawo Matsaloli Masu tarin yawa a jikin Dan Adam.

 

Da take jawabi yayin taron Sa’adatu Nuhu Wali Wacce ita ce shugabar kungiyar a nan Kano tace sun shirya taron ne domin wayar da kan al’ummar Arewacin Kasar nan dangane da muhimmancin zuwa asibiti domin duba lafiyarsu, Inda tace al’umma da dama suna fama da Wannan cuta ta amosanin Kashi amma basu saniba .

 

Tace al’umma da dama su kan alakanta wanann cuta da cutar sickler ba tare da sun je an gwada su ba.

 

Sa’adatu Wali ta kara da cewa yawancin masu fama da wannan cuta matane marasa karfi ,don haka tace suka kafa kungiyar domin tai makawa masu fama da larurar.

 

Wakilinmu Kadaura24 ya ruwaito Cewa taron ya sami halartar shugaban karamar hukumar gaya alh. Ahamad Tijjani Abdullahi wanda yasami wakilcin Nura Bello Gaya, da kuma Dr. Bala Ladan shugaban sashin ilmin manya da kuma masu bukata ta musamman na kwalejin sa’adatu rimi, daliban makarantar GGSS Gidan makama da na GGSS Gaya Dana makarantar yan mata ta Zahra na nono da dai Sauransu.