Daga Abubakar Yakubu Abubakar
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya koka kan rasuwar Alhaji Muhammad Aminu Adamu wanda aka fi sani da Abba Boss.
Cikin Wata sanarwa da Abba Anwar Mai Magana da yawun Gwamnan ya aikowa Kadaura24 yace Gwamna Ganduje ya bayyana marigayin a matsayin fitaccen shugaba na gari, uba na ainihi ga mutane da yawa da suka zauna tare da shi, mai tarbiyya kuma ɗan tarbiyya, wanda ya yi imani da hidimtawa Rayuwar al’ummar .
Ya kara da cewa, “Wannan mutuwa, ta zo ne lokacin da muke matukar bukatar sa, Saboda Mutum ne Mai karamci.
Gwamna Ganduje ya ba da tabbacin cewa, marigayi Abba Boss, ɗan Najeriya ne mai kishin ƙasa, wanda ya damu ƙwarai da ci gaban al’ummarsa, jiharsa da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya kara da cewa, “babu shakka ya rasu yayin da muke bukatarsa, amma Allah Madaukakin Sarki ya fi son shshi muna addu’ar Allah yasa kyawawan ayyukan su bishi”.
“Don haka a madadin gwamnati da mutanen jihar Kano, ina mika ta’aziyyar mu ga iyalan Alhaji Muhammad Aminu Adamu, makusantan sa, abokan sa, masu son sa da sauran al’umma baki daya. Allah Ya gafarta masa dukkan kurakuran sa. kuma ya saka masa da kyawawan ayyukansa da Jannatul Fiddaus, ”in ji gwamna.