Gwamna Ganduje ya aike da ta’aziyyar rasuwar Muhammad Aminu Adamu (Abba Boss)

Date:

Daga Abubakar Yakubu Abubakar
 Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya koka kan rasuwar Alhaji Muhammad Aminu Adamu wanda aka fi sani da Abba Boss.
 Cikin Wata sanarwa da Abba Anwar Mai Magana da yawun Gwamnan ya aikowa Kadaura24 yace Gwamna Ganduje ya bayyana marigayin a matsayin fitaccen shugaba na gari, uba na ainihi ga mutane da yawa da suka zauna tare da shi, mai tarbiyya kuma ɗan tarbiyya, wanda ya yi imani da hidimtawa Rayuwar al’ummar .
 Ya kara da cewa, “Wannan mutuwa, ta zo ne lokacin da muke matukar bukatar sa, Saboda Mutum ne Mai karamci.
 Gwamna Ganduje ya ba da tabbacin cewa, marigayi Abba Boss, ɗan Najeriya ne mai kishin ƙasa, wanda ya damu ƙwarai da ci gaban al’ummarsa, jiharsa da ma ƙasa baki ɗaya.
 Ya kara da cewa, “babu shakka ya rasu yayin da muke bukatarsa, amma Allah Madaukakin Sarki ya fi son shshi muna addu’ar Allah yasa  kyawawan ayyukan su bishi”.
 “Don haka a madadin gwamnati da mutanen jihar Kano, ina mika ta’aziyyar mu ga iyalan Alhaji Muhammad Aminu Adamu, makusantan sa, abokan sa, masu son sa da sauran al’umma baki daya. Allah Ya gafarta masa dukkan kurakuran sa.  kuma ya saka masa da kyawawan ayyukansa da Jannatul Fiddaus, ”in ji gwamna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...