Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano PCACC ta bankado tare da rufe wasu shaguna da dama da ake zargin an boye tarin kayan masarufi a wasu kasuwannin jihar.
Kadaura24 ta rahoto cewa a ranar Lahadi hukumar ta gudanar da wani samame karkashin jagorancin shugabanta Muhuyi Magaji Rimin-Gado zuwa wasu rumbunan ajiya.
Allah Ya Yiwa Guda Cikin Jaruman Fim din Dadin Kowa Rasuwa
A yayin samamen, rundunar ta bankado wasu rumfuna kusan 10 da ke jibge kayan masarufi a kasuwar hatsi ta Dawanau da kuma kasuwar Singer.
Naburaska ya Magantu Kan Masu Kokarin Hana shi Shirya fim din IGIYAR ZATO
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar Alhamis din data gabata shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bada sanarwar cewa hukumar zata fara ran gadin Kama yan Kasuwa dake boye kayan masarufi tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Al’ummar Nigeria dai sun shiga halin kakanikayi sakamakon tsadar kayan Abinchi, wanda ake ganin hakan yana da alaka da tsadar dalar Amuruka da kuma yadda wasu yan Kasuwar suke boye kayan masarufin don cin kazamar riba.