Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Kungiyoyin kwadago a Najeriya NLC da TUC sun baiwa gwamnatin tarayya wa’adin Kwanaki 14 ta cika alkawurin da suka kulla ko su tsunduma yajin aiki a fadin Kasar.
Koken nasu ya samo asali ne daga rashin aiwatar da yarjejeniya 16 da aka kulla tsakanin kungiyoyin kwadago (NLC da TUC) da gwamnatin tarayya a ranar 2 ga Oktoba, 2023.
Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano ta Bayyana Yadda Zata Yaki Yan Kasuwa Masu Boye Kayan Masarufi
Shugabannin kungiyoyin NLC da TUC sun bayyana damuwarsu da cewa, duk da kokarin da kungiyoyin kwadago ke yi na inganta zaman lafiya a ma’aikatu, ga dukkan alamu gwamnati ba ta damu da wahalhalun da al’umma suke ciki ba .
Tsadar Kayan Abinchi: Kotu Ta Baiwa Gwamnatin tarayya Umarni
NLC da TUC, a cikin wata sanarwa da suka fitar, sun koka da cewa “abin takaici ne yadda aka tilasta mana daukar irin wadancan matakan, amma rashin kula da walwalar ‘yan kasa da ma’aikatan Najeriya da kuma tsananin wahala ya sa ba mu da zabi sai mun yi haka.”
“Sakamakon wannan ci gaba tare da sanin muhimmancin tabbatar da tsaro da kare hakki da mutuncin ma’aikatan Najeriya da ‘yan kasa, kungiyar NLC da TUC sun ba da wa’adi ga gwamnatin tarayya da ta mutunta yarjejeniya cikin kwanaki 14 daga gobe, ranar 9 ga Fabrairu 2024.”