Yadda Matasa a Kano suka gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Nigeria

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Matasa maza da mata da dama a jihar Kano sun sufi domin gudanar da zanga-zanga, don nuna adawarsa da tsadar kayan masarufi da ake fuskanta a Nigeria .

Masu Zanga-zangar dai sun fito ɗauke da kwalaye, inda suke rera waƙa mai taken “Tsadar Rayuwa ba zamu iya ba”, a ƙoƙarin da suke yi na nunawa da nu halin da suke ciki.

Matasan waɗanda suka futo fuskokinsu a murtuke, sun gudanar da zanga-zangar ne yau Alhamis a unguwannin Bachirwa, Kurna da kuma Rijiyar lemo, dake kan titin zuwa katsina a Kano.

Da dumi-dumi: Kungiyar Kwadago ta Bayyana Ranar Fara Yajin Aiki a Nigeria

Haka kuma Masu Zanga-zangar dai sun ce Rayuwar tayi musu matuƙar wahala, a sakamakon yadda abinci yake neman gagararsu, balle aje ga sauran Buƙatu na Rayuwa.

Baya ga haka sunce kayan masarufi yana neman gagararsu, saboda yadda abubuwa da yawa suka ninka kuɗin su sama da sau biyar, wasu mah Sai goma.

Jinkirin biyan albashi: Ma’aikatan gwamnati sun kalubalanci Tinubu

Adan haka suka fito zanga-zangar, dan nuna fushin su da salon kamun ludayin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, duba da yadda yake neman kassara Rayuwarsu.

A ƙarshe sunyi fatan dukkan masu ruwa da tsaki zasu yi dukkan abubuwan da suka kamata, domin kawo wa Talakawan Najeriya ɗauki daga wannan hali da suke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...