Daga Ibrahim Sani Gama
Kungiyar kasuwar Singa wato (SEMEDAN) ta jaddada kudirinsa na inganta lungu da sako na kasuwar domin saukakawa al’umma da kuma cigaban kasuwar baki daya.
Sakataren Kungiyar Ibrahim Nafi’u Abdullahi Mentos ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai Jim kadan bayan kaddamar da fara gyaran titunan dake fadin kasuwar.
“Kungiyar yan kasuwar da hadin gwiwar wasu Dattijan kasuwar ne, suka hada hannu wuri guda domin gudanar da aiki, kasancewar an kwashe tsawon lokuta da tsuhuwar kungiyar ta gaza yi, amma da zuwan wannan sabon Shugabancin yayi ayyuka da dama a cikin kasuwar singa”. A cewar Ibrahim Nafi’u.
Gobara ta Kone Kayan Abinchi da Dabbobi a Kano
Ibrahim Nafiu Abdullahi yace Kungiyar ta samar da motar kashe gobara, sannan kum yanzu tana da aniyar aiwatar da ayyuka daban-daban da za su inganta kasuwanci da taimakawa marasa karfi da suka hada da yandako da mayar da ‘ya’yan marasa karfi zuwa makarantu domin inganta rayuwarsu kamar kowa.
Ya bayyana cewa, Kamfanoni da dama da suke mu’amulla da yan kasuwar sun sha alwashin ba da tasu gagarumar gudunmawar wajen inganta lungu da sako na kasuwar Singa yadda ya kamata.
Ƙaranci Sadaki: Mal Ibrahim Khalil ya kalubalanci Batun Naira 100, ya fadi hakikaninsa
Ibrahim mentos ya kara da cewa, Kungiyar ta yabawa wadan nan Kamfanoni da suke ba da wannan gudunmawa ta yau da kullum wajen tabbatar da kasuwanci ya samu gagarumar nasara a fadin jihar kano da kasa baki daya.
Haka zalika Kungiyar kuma, yabawa Dattawan wannan kasuwa da suka hadar da Alh Salisu Sanbajo Alh. Adakawa da sauran Yankasuwar da suke ba da gudunmawa wajen ganin kasuwanci jihar kano da kasa ya ci gaba da rike kanbunsa yadda ya kamata,kasancewar jihar kano cibiya ce ta kasuwanci.
Kungiyar ta kuma ce kofarta a bude take wajen bayar da shawarwari da gudunmawa wajen inganta lungu da sako na cikin kasuwar kwanar Singa dake nan birnin kano.