Kotu ta sanya ranar saurarar karar da aka shigar don kalubalantar hukuncin da aka yanke wa Abduljabbar

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Wani Musa San Turaki Fali almajiri kuma mabiyin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara a Bauchi ya shigar da kara a gaban babbar kotun jihar Kano.

Mai shigar da kara, ta bakin lauyan sa, Barista Hashim Hussain Fagge yana neman izinin shigar da kara domin kalubalantar hukuncin kisa da kotun shari’ar Musulunci ta Kano ta yanke a Kofar Kudu.

Soja ya bude wuta, ya kashe ogansa, ya raunata wasu a Sokoto

Jaridar kadaura24 ta rawaito cewa kotun dake Kofar kudu a ranar 15 ga Disamba, 2022, ta yanke wa Abduljabbar Nasir Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin fadin kalaman da basu dace ba akan manzon Allah (S A W).

Justice Watch News ta rawaito Mai shigar da kara, Fali, ya shaida wa kotun cewa ya shigar da karar ne bisa dogaro da sashe na 272 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.

Tsadar Kayan Abinchi: Zanga-Zanga Ta Barke A Jihar Neja

A zaman da aka yi a yau litinin, Barista Musa Dahuru Muhammad, lauyan gwamnatin jihar Kano, ya shigar da bukatar a kara masa lokaci domin mayar da martani akan bukatar kalubalantar hukuncin da kotun shari’ar musulunci ta yanke.

Hakazalika, lauyan da ke kare Hashim Fagge ya kuma bukaci a dage shari’ar a madadin wanda yake karewa, domin ba shi damar mayar da martani kan karar gwamnatin jihar Kano.

Bayan nazarin dukkan bangarorin biyu, Mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu domin sauraron karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...