Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Wani tsohon dan takarar gwamnan jihar kano Alhaji Sanusi Rabi’u Ƙoki ya koka dangane da kalaman malamin jami’ar nan Farfesa Tijjani muhd Naniya Wanda ya bayyana cewa zauren dattawan Kano da gwamnan kano zai kafa ba zai haifar da da mai ido ba.
” Bamu ji dadin kalaman da Farfesa Tijjani muhd Naniya yayi akan zauren dattawan Kano ba, saboda irin alfanun da samar da zauren zai yi ga al’ummarmu da jihar kano baki daya”.
Siyasar Kano: Tinubu Ya Baiwa Kwankwaso da Ganduje Umarni
Alhaji Sanusi Koki ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 a Kano.
Yace bayan ga hada zan shugabannin jiha kano, Zauren zai rika tallafawa gwamnatin jiha da shawarwarin da zasu inganta rayuwar al’umma jihar kano ta kowacce fuska, saboda yadda aka sanya muhimman mutane cikin zauren .
Rashin Tsaro: Gwamnatin Filato ta Sanya Dokar Hana Fita
“Ina baiwa al’ummar jihar kano shawarar su ajiye maganganun da Naniya yayi, saboda duk lokacin da aka zo za’a yiwa al’umma wani abun alkhairi bai kamata wani ya fito ya rika sukar shi ba, ai wadancan mutane da za’a tara shawara zasu rika baiwa gwamna , kuma ko addinin mu ya bukaci shugabanni su rika neman shawara saboda haka manzon Allah S A W ya rika yi”. Inji Sanusi Koki
Yace ya kamata malaman jami’a a kowanne lokaci su rika yin tunanin yadda abun da aka kawo don cigaban al’umma ya taimaki al’ummar ba wai su rika suka ko fadar matsaloli ba, saboda kowanne abu yana da amfani da rashin amfaninsa, amma kamata yayi indai amfanin abu yafi yawa to aiwatar da shi kawai”.