Da dumi-dumi : Ganduje ya Sanar da Sunan Sabon Sarkin Gaya

Date:

Daga Usman Hamza

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Amince da nadin Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a Matsayin Sabon Sarkin Masarautar Gaya, bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Alhaji Ibrahim Abdulkadir.

Sakataren Gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ne ya bayar da Sanarwar a madadin gwamnatin jihar Kano.

Kadaura24 ta rawaito cewa gabanin bayar da Sanarwar Sabon Sarkin, sai da Masu zabar Sarki a Masarautar Gaya suka gudanar da aikinsu na zabar Sarki kafin daga bisani gwamnan Kano ya Amince da Sabon Sarkin na Gaya.

Gwamna Ganduje ya zabi Alhaji Aliyu Wanda da shine ciroman Gaya Kuma babban da ga Marigayi Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir na cikin Mutane uku da Masu zabar Sarki a Masarautar suka gabatar Masa a Matsayin Waɗanda suka zaba

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Marigayi Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir ya Rasu a Ranar Larabar nan data gabata.

39 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...