Matasan Nigeria na goyon Bayan Yari A Shugabancin APC na Kasa – Com. Auwal Dalhatu

Date:

Daga Halima M Abubakar

Shugaban Kungiya Yan Damuwar ‘yan ƙasa masu tunani iri daya na kawo cigaba a jam’iyyar APC Wato Concerned Citizen and like mainds sun bayyana Cewa Babu Wanda ya dace da Shugabanci jam’iyyar APC a matakin Kasa face Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz yaro Shattiman Zamfara.

Kadaura24 ta rawaito Com. Auwal Dalhatu Sani ne ya bayyana hakan yayin Wani gaganmin taron Matasa maza da mata Masu akidar Siyasar Abdulaziz Yari, taron Wanda ya gudana a birnin Kano.

Com.Auwal Dalhatu yace halin da jam’iyyar APC take Ciki a Wannan Kasa Babu mai iya Magance Matsalar sai Abdulaziz Yari , Saboda irin kwarewar da yake da ita a sha’anin Siyasa da Shugabanci.

“Mun San irin aiyukan alkhairi
na Raya Kasa da cigaban al’umma da Abdulaziz Yari ya gudanar a Zamfara,Haka mun shaida yadda ya rike Kungiyar Gwamnonin Kasar nan don Haka muke ganin Yari shi Kadai ne Zai iya Kai jam’iyyar APC ta Kasa zuwa Tudun muntsira.” Inji Com. Auwal Dalhatu

Com. Auwal Dalhatu Sani yace Abdulaziz Yari yana da manufofi managarta Waɗanda zasu taimaka matuka Wajen Daga darajar jam’iyyar APC a Nigeria.

” Abdulaziz Yari Abubakar Mutum ne da ya ke da tausayi Kuma yake da burin ganin Matasa sun Sami ingantacciyar rayuwa, don Haka Matasan Kasar nan suke goyon Bayan Hon. Abdulaziz Yari ya Zama Shugaban jam’iyyar APC a Nigeria.” Inji shi

Shugaban Kungiyar yayi fatan al’ummar jihar Kano Musamman yan jam’iyyar APC zasu fito kwansu da kwarkwata don Mara baya ga Abdulaziz Yari ya Zama Shugaban jam’iyyar APC na Nigeria.

19 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...