Daga Abubakar Lawan Bichi
Dan majalisar tarrayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi, wanda kuma Shugaban kwamiti kasafin kudin na Majalisar wakilai Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi ya baiwa Daliban Makarantun Kimiyya da Fasaha na Jahar Kano Mazauna Karamar hukumar Bichi su (547) Kudin Guzirin Komawa hutu zango Karatu na biyu.
Kadaura24 ta rawaito Kudin da Abubakar Kabir ya basu ya kai Nera Miliyan takwas da dubu dari bakwa da biyar (8,705,000) , inda kowanne dalibi ya rabauta da Nera dubu 15 ta Karkashin Gidauniyar Kabir Abubakar Bichi.

Dan Majalissar wanda ya sami wakilcin Shugaban ma’ikatansa Alhaji Sabo Iliyasu Saye ya yi kira da daliban da su zama wakilan karamar hukumar Bichi na gari wajan maida hankali a Karatunsu.
Gaskiyar Batu Kan Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Gwamnan Kano
Hon Sabo Saye ya Sanarwa daliban cewa Dan Majalisar yace zai cigaba da daukar nauyi Karatu dalibai yan asalin karamar hukumar Bichi har zuwa digirin na Uku,
A Jawabinsa mai taimakawa Dan Majalisar Tarrayya Mai wakiltar Karamar hukumar Bichi akan harka Ilimi Zaharradeen Bello Bichi yace nan gaba kadan dan Majalisar zai fara daukar nauyi Karatu daliba yan asalin karamar hukumar Bichi zuwa Kasashen wajen domin Karo Karatu.
Taron yasami halattar iyayan yara, da Ma’aikata Dan Majalissar, da dattawan jamiyyar APC.