Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gamayyar kungiyoyin farar hula na Arewacin Nigeria sun bukaci shugaban Kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu da tabbatar an yi adalci a shari’o’in gwamnonin Kano da Zamfara saboda gudun abun da zai kawo ruɗani a cikin al’umma.
“Al’ummar wadancan jihohi sun zabi wadanda suke so a lokacin zabe a matsayinsu na yan kasa, to ya kamata a mutunta abun da suka zaba, ayi musu adalci kada ayi amfani da kotuna wajen yi musu abun da zasu ji cewa ba ayi musu adalci ba”.
Shugaban Gamayyar kungiyoyin Amb. Ibrahim Wayya ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar lahadi a Kano.

” Adalci shi ne kashin bayan zaman lafiya a cikin kowacce al’umma, kuma rashin yin adalcin ya kan kawo ruɗani a cikin al’umma, don haka muna kira ga mai girma shugaban kasa da kada ya bari a karkashin mulkinsa a tauyawa mutane hakkinsu na dimokaradiyya”. A cewar Waiya
Kamfanin Ɗangote ya Bayyana Dalilin Da Ya Kai EFCC Ofishin Su Dake Legos
Amb. Ibrahim Waiya ya kuma bukaci shugaban Kasar da ya dauki matakan da suka dace wajen kawo karshen matsalolin tsaron da ake fuskanta a wasu jihohin arewacin Nigeria, da wasu sassan Kasar baki daya.
” Matsalolin rashin tsaro suna kara yawa a Nigeria don haka muna baiwa shugaban kasa shawarar ya samar da wata kafa da zai rika tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaro don auna kokarinsu da kuma daukar matakan da suka dace akan duk wanda ya gaza da kuma yabawa wadanda suka yi bajinta a cikin su”. Inji Ibrahim Waiya
AAPU ta Yabawa Ministan Ilimin Nigeria, Bisa Daukar Matakin Bincikar Shaida Digiri Dan Kwatano
Yace a wannan lokaci da al’umma suke cikin matsanancin talauci, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dauki matakan da suka dace don gudun kada Abubuwa su yiwa yan kasa yawa su zo su tunzura su aika abun da bai dace ba.
” Muna yabawa gwamnonin jihohin Kaduna, Zamfara, Sokoto, Katsina da Barno saboda kokarin da suke yi wajen yaki da matsalolin tsaro a jihohin su, sannan Muna fatan shugaban kasa Tinubu da shugabannin hukumomin tsaro zasu tashi tsaye wajen yakar matsalolin tsaro.