Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta rufe asusun ajiyar kudi na kasa wato (TSA) da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi amfani da shi wajen tara kudaden shiga.
Sai dai gwamnatin tarayya ta umurci dukkan ma’aikatu, da hukumomi da su tura kashi 100 na kudaden shiga zuwa asusun ajiyar kudaden shiga na yau da kullun, wani bangare na asusun tattara kudaden shiga (CRF).
Hukumar Tace Fina-Fina ta Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Zargin da ake yiwa Jaruma Maryam Yahya
CRF shine sabon asusu inda a yanzu gwamnatin Tinubu za ta karba tare da hada kudaden shigarta a cikin sa.

Hakan ya zo ne bisa wata takardar da mai kwanan watan 28 ga Disamba, 2023, wadda ma’aikatar kudi ta fitar a ranar Talata, 2 ga Janairu, 2024.
Wannan umarni dai ya rufe asusun baitul mali na bai daya da tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi amfani da shi.