Wakokin Kannywood 5 Da Suka Fi Shahara A 2023

Date:

 

  1. A kullum, idan aka ce fitattun waƙoƙin Hausa na shekara, ana nufin waƙoƙin da aka fi saurare a kafafen yaɗa labarai kamar rediyo, talbijin da soshiyal midiya.

Sauyawar zamani ya sanya waɗannan waƙoƙin su ne na zamani da ake buga su a situdiyo da kiɗan fiyano ko haɗin fiyanon da kalangu, ba na gargajiya irin na su Shata da Ɗanƙwairo ba.

A 2023 ma, kamar kowace shekara a wannan zamanin, waƙoƙin fiyano su ne aka fi saurare a kafafen yaɗa labarai. A binciken da muka yi, mun gano cewa a bana waƙoƙin soyayya ne suka mamaye fagen, kuma maza ne suka riƙe kambin a cikin waƙoƙi guda 5 mafi fice da aka samar.

Ga su kamar haka:

1. Sauti – Ado Isah Gwanja

 

Ado Gwanja

Sauti’ waƙa ce a jerin salon waƙoƙin da Ado Isah Gwanja yake yi a yanzu, wanda kusan ita ce ta biyar a cikin irin wannan waƙoƙi na salon habaici, tun daga kan waƙoƙin ‘Warr’, ‘Cass’, ‘Iye’, ‘Luwai’, sai kuma ita ‘Sauti’.

A cikin duk waɗannan waƙoƙin, ‘Warr’ da ‘Cass’ sun yi fice a shekarar da ta gabata.

Musamman ganin mawaƙin ya zo da sabon salo, wannan ya sa jama’a suka so waƙoƙin, wanda har sai da ta kai an hana saka waƙoƙin a gidajen rediyo, wasu lauyoyi suka yi ƙarar mawaƙin a kotu.

Amma kuma sai ya zama kai ka ce an ƙara wa Gwanja fiƙira ne, domin kuwa ya ci gaba da sako irin waɗannan waƙoƙin, har zuwa wannan mai suna ‘Sauti’, wadda yanzu watan ta uku da saki.

Baitin da ya ɗauki hankalin jama’a, ya yi yawo musamman a TikTok, wanda a yanzu a can ake baza waƙoƙi, shi ne:

‘Turmi ya cashi tsaki, a banza, a banzazza!

Talaka ya girmi sarki, a banza, a banzazza!

Kaska ta zagi kifi, a banza, a banzazza!

Ɗaki babu murfi, a banza, a banzazza!

Barazana babu ƙarfi, a banza, a banzazza!”

2. Rayuwa Ta – Umar M. Shareef da Zubaida Mu’azu

Umar M Shareff

Rayuwata, waƙa ce ta soyayya tsakanin saurayi da budurwa. A cikin ta, gwanayen mawaƙan nan Umar M. Shareef da Zubaida Mu’azu sun nuna ƙwarewa wajen karya murya da kuma zuba kalmomi na shauƙi.

Waƙar ta yi fice a soshiyal midiya, musamman a TikTok, inda za ka ga budurwa ta ɗauki bidiyon kanta, ta kuma saka hoton masoyinta a jiki tana bin kalaman da mawaƙan suke rerawa tare da nuna shauƙin soyayya.

Baitin da ya kama zuciyar masoya a waƙar shi ne:

“Na samo yarinya kyakkyawa,

kun gan ta son kowa, ta sa min jin daɗi.

In ta fito, kowa na rububi gun kallonta ya yi ta rawa a jikinsu suna kauɗi”.

Ita ma macen sai ta maimaita abin da namijin ya faɗa.

Sai ya ƙara da cewa:

“Da Turanci in zan kira ki, darling tsarina,

da Larabci ƙurratu ainun, sanyi na idona,

Faransanci monafur, shi ne zaɓina,

kin zarce yadda suke tunani a cikin raina.”

Ita kuma sai ta ce:

“Da Turanci in zan kira ka, Babyna,

da Larabci kuma sannu nurul ƙalbina,

Faransanci masheri, abin ƙauna,

ka zarce yadda ake tunani a cikin rai na.”

Wan mawaƙin, wato jarumi Abdul M. Shareef, da jaruma Maryam Malika ne suka yi bidiyon waƙar.

3. Aisha – Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) da Zuwaira Isma’il

Dauda Kahutu Rarara

Waƙar ‘A’isha’, an saka ta ne a fim ɗin ‘A Cikin Biyu’ na jaruma A’isha Ahmad Idris (A’ishatulhumaira).

Sanannen mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ne ya rera ta tare da fitacciyar zabiya Zuwaira Isma’il.

Mawaƙin ya yi wa mutane bazata domin ba a taɓa jin waƙar soyayya daga wurin sa ba sai a wannan karon. Waƙar ta ɗauki hankalin mutane sosai, har ta kai ana yaɗa ji-ta-ji-tar zai auri A’isha Humaira ne, wadda tana ɗaya daga cikin manyan muƙarrabansa a Kannywood.

A waƙar, Rarara ya zo da wani salo da ya sha bambanta da sauran waƙoƙin soyayya.

Ya yi amfani da kalamai masu ratsa zuciyar duk wata mace da ke cikin shauƙin soyayya.

Waƙar ta yaɗu a soshiyal midiya, musamman a lokacin da ake ɗaukar fim ɗin ‘A Cikin Biyu’ a Jihar Jigawa. Jaruman fim ɗin su ne Ali Nuhu, Adam A. Zango da ita A’ishatulhumaira.

4. Halitta – Nazifi Asnanic

Nazifi Asnanic

 

Halitta, waƙar soyayya ce inda mawaƙin ke siffanta halittar masoyiyarsa.

Nazifi Asnanic ya gigita masoyan zamani da wannan waƙa.

Ya yi amfani da kalmomi masu cafke zuciya ta yadda duk macen da take cikin nishaɗi irin na soyayya sai ta ji kamar ita ake furta wa kalaman da take saurare daga bakin mawaƙin.

Nazifi ya ƙalubalanci abokansa mawaƙa a kan wannan waƙa, inda ya yanki amshin waƙar da baiti ɗaya, daga nan kuma sai duk wanda zai yi baitinsa, sai ya ɗauka shi ma ya yi, sai ya ɗora a soshiyal midiya.

Manyan mawaƙa da ƙanana sun yi. Wannan ya ƙara fitar da waƙar, ta yaɗu sosai.

5. Farin Ciki Na – Auta Waziri da Shamsiyya Sadi

Auta Waziri

Ita ma ‘Farin CikiNa’ waƙar soyayya ce.

Mawaƙan sun yi amfani da kalmomi masu taɓa zukatan matasa matuƙa. Waƙar ta yi fice sosai, kuma ta yi tasiri musamman a wajen masoya.

Duk inda ka shiga a soshiyal midiya za ka ga maza da mata suna amfani da ita, saboda kalaman da aka yi amfani da su.

Auta ba sabon mawaƙi ba ne, amma yana ɗaya daga cikin masu tashe a yau.

A baya waƙoƙin sarauta da siyasa da ire-irensu ya fi mayar da hankali a kai, amma sai ya rikiɗe ya koma waƙoƙin soyayya.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...