Mun haramta nunawa ko sayar fim din da ake Garkuwa da Mutane a Cikin sa – Afakallah

Date:

Daga Aisha Muhd adam

Hukumar Tace Finafinai ta jihar Kano, ta haramta nunawa ko sayar da fina -finan da ke nuna garkuwa da mutane, shan muggan kwayoyi da kwacen wayoyi a Cikin su a jihar Kano.

Sakataren zartarwa na hukumar, Ismaila Naaba Afakallah, ya bayyana cewa haramcin ya zama tilas, saboda abubuwan da ake magana yanzu sun zama sanannu a tsakanin Jama’a Kuma suna taimakawa Bata gari.

“Daga yanzu, ba za mu amince da fina -finan da ke nuna garkuwa da mutane ba, shan muggan kwayoyi da wayoyin GSM wanda yanzu ya yi wa al’ummar jihar Kano illa”.

Afakallah ya bayyana cewa an dauki matakin ne don takaita barazanar da kuma rage yiwuwar matasa su yi amfani da Hanyoyin wajen shiga aiyukan da basu dace ba.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...

Gwamnatin Kano ta magantu kan Hukuncin kotu na zaben kananan hukumomi

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Kano ta bayyana farin...