Sojoji sun ceto Manjo CL Datong, wanda yan bindiga suka sace daga Makarantar Tsaro ta Najeriya (NDA) kwanaki 21 bayan faruwar lamarin.
An yi garkuwa da babban jami’in ne bayan da ‘yan bindiga suka kutsa kai cikin hukumar NDA inda suka kashe jami’ai biyu.
Da yake ba bayyana yadda aka kubutar da shi, rundunar sojin Najeriya a cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar ta 1 ta sojojin Najeriya, Kanal Ezindu Idimah, ya ce rundunar sojojin Najeriya tare da rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) da dukkan hukumomin tsaro sun sun gudanar da wani gagarumin aiki hadin don kubutar da Manjo.
Ya bayyana cewa bayan rusa sansanin ‘yan ta’adda da dama da aka gano a yankin Afaka- Birnin Gwari tare da kashe’ yan ta’adda da yawa, sojoji sun isa sansanin da ake zargi shine wurin da ake tsare da Maj CL Datong