Ku baiwa Jami’an Lafiya hadin Kai don Magance Polio – Shugaban K/H kumbotso

Date:

Daga Aisha Muhd adam

Shugaban karamar hukumar Kumbotso Hon Hassan Garban kauye farawa ya Bukaci Al’ummar yankin dasu baiwa jami’an lafiya dake Aikin Allurar Riga-kafin Shan Inna Hadin Kan daya dace domin ceto Rayuwar Yara kanana dake fuskantar Barazanar wannan cuta.

Shugaban ya Kuma yabawa kokarin Gwamantin Kano karkashin jagorancin Gwamnan Dr Abdullah Umar Ganduje na yaki da cutar Shan Inna a karamar hukumar Kumbotso dama jiha Baki daya.

Kazalika Farawa ya Kuma jinjinawa ma’aikatar lafiya ta jihar Kano bisa yadda take aiki ba Dare ba Rana Domin kula da lafiyar al’umma tun daga matakin farko da Kuma yaki da wannann cuta ta polio a Turance.

Garban kauye ya Kuma Mika sakon godiya ga Mai girma Mataimakin Gwamnan Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna bisa yadda yadda jagoranci kaddamar Da Gangamin Shirin yaki da cutar Shan-Inna da sauran cuttuka dake addabar yara kanana Wanda ya gudana garin Mariri Cikin yankin karamar Hukumar Kumbotso, Bisa Wakilcin Shugaban Hukumar CPC na jihar Kano Rt Hon Ya’u Abdullah Yan Shana.

“Hon Garban kauye ya Bukaci iyayen kasa Dagatai da masu unguwanni dasu baiwa jami’an Hukumar lafiya dake aikin Allurar Rigakafin Hadin Kan Daya Dace dama sauran Al’ummar yanki Baki Daya, akokarin gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamnan Dr Abdullah Umar Ganduje da Gwamnatin Tarayya da sauran kungiyoyin Duniya na yaki da wannan Cuta”.

Sannan Kuma yaja Hankalinki al’umma r yankin dasu kula da lafiyar abincinsu da Ruwan Sha Domin kaucewa Annovar Ami da Gudawa da sauran cuttuka, Wannana dai kunshe Cikin wata sanarwa da shugaban karamar hukumar Kumbotso ya fitar dauke dasa hannun Maitaimakasa Kan harkokin yada labarai muhamamd Shazali farawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...