Kwankwaso ya Fadi yadda Suka hadu da Ganduje a filin Jirgin Sama

Date:

A karon farko, tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana yadda haɗuwarsa ta kasance da abokin takun saƙarsa na siyasa, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a filin jirgin saman Abuja, babban birnin Najeriya.

Sanata Kwankwaso ya shaida wa BBC Hausa cewa ya riga Gwamna Ganduje zuwa filin jirgin da kamar awa guda, a lokacin ne ya samu labarin cewa shi ma magajin nasa na kan hanyar isowa filin jirgin.

“Na ce to Allah ya kawo shi, kasuwa ce ai kamar tasha ce, ba wanda za ka ce ya zo ko kar ya zo, muka shiga jirgi daya da shi muka taho, muka sauka a wanan tasha ta Kano, na kama hanyata ya kama tasa ya tafi gida.”

Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ”A matsayi irin na Musulunci ai ba lallai sai kana jam’iyya daya da mutum za ka gaisa da shi ba, mun gaisa da shi kowa ya koma ya zauna a kujerarsa, don haka haka muka isa har Kano kowa na zaune a kujerarsa.

Kadaura24 ta rawaito tun Bayan da aka Sami sabani tsakanin Kwankwaso da Ganduje Wannan ne karon Farko da Suka gaisa da juna ,duk da abaya sun gadu a wuraren taro Amma kowa bai gaisa da Dan uwansa ba.

79 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...