Daga Halima M Abubakar
Hukumar Kare hakki Masu Siya da Masu sayarwa ta jihar Kano ta ce ta kuduri aniyar kare masu siyayya ta hanyar rage yaduwar jabun kayayyakin da wa’adin su ya kare.
Kadaura24 ta rawaito Sabon Manajan Darakta na Hukumar Birgediya Janar Idris Dambazau RTD ne ya bayyana hakan a lokacin da yake Zantawa da Manema labarai a kano.
Ya ce Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kama duk wadanda ke harkar sayar da kayayyakin da wa’adin suka kare da Kuma na jabu.
Idris Dambazau ya bayyana cewa a lokacin da ya zama sabon Manajan Daraktan hukumar, ya zo da Tsare-tsaren da suka dace don magance matsalar.
Manajan Daraktan yace wadanda ke aikata irin wannan munanan ayyukan su sani ba su da mafaka a jihar Kano, yana mai cewa ma’aikatan sa sun dukufa wajen tabbatar da an kamo wadanda suka aikata wannan aika -aika don gurfanar da su a gaban kuliya.
https://night-lady.co.il