A Shirye Mu ke Don yakar Dabi’ar tura ‘ya’ya Mata aikatau zuwa Birane – Kungiyar Isa Wali

Date:

Daga Safiya Dantala Jobawa

Wata kungiya Mai Zaman kanta Mai Suna Isa Wali Empowerment Initiative ta shirya wani gangamin mata da a Garin Jobawa da nufin yaki da tura yara mata birane karkashin jagorancin Dagacin garin jobawa a karamar hukumar Garun malam jihar kano malam Umar Inuwa domin wayar da kan al’umma musammam ma mata akan tura yaransu mata aikatau watau.

Kadaura24 ta rawaito Matan sun sha alwashin zakulo iyayen da suka bujire wa hukuma tare da fallasa su domin nema wa mata yanci daga bautar da su da Sunan aikatau.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar Isa Wali Empowerment Initiative (IWEI). Barrister Hafsat zeenat ta ce “sun sami labarin wasu iyaye na tura ‘ya’yansu mata yin aikatau wanda hakan bai dace ba sam a wannan zamani da ake samun bata gari masu yi wa mata fyade, da sauransu.

Barr. Zeenat nan take a gaban dubun nan mata ta ce “za su dafa wa matan yankin da wasu dabarun da Hanyoyin da zasu bi domin dogaro da kai maimaikon tura ‘ya’yansu Birni da Sunan aikatau.

Shugaban karamar hukumar Garun malam Alh Mudansir Dakasoye, ya gode wa wannan kungiya ta ISA WALI KANO tare da dagacin Jobawa da kansilan jobawa Hon Abdullahi Ba matsala a bisa wannan yunkuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...