Shugaban K/H Rano ya Sanya Dokar Hana Zancen dare Tsakanin Saurayi da Budurwa a Rano

Date:

Daga Safiyan Dantala Jobawa

Mahukuntan karamar hukumar Rano da ke Jihar Kano a sun bijiro da wata sabuwar doka da za ta hana zance ko hirar dare tsakanin Saurayi da budurwa da ma zawarawa.

Mahukuntan sun ce sun sanya wannan doka ne tsakanin masu neman aure a faɗin yankin da zummar kawo tsafta tsakanin matasan yanki.

Wata sanarwa da shugaban karamar hukumar Rano ya fitar Alhaji Dahiru Muhammed Ruwan Kanya, ya ce an dauki matakin ne ganin yadda cikin shege ya yawaita da gurbata tarbiyya tsakanin masu zance da sunan neman aure.

Wannan mataki dai ya haifar da maban-banta ra’ayi a yankin, ko da yake galibin iyayen yara da wasu matasa na ganin hakan ya dace.

Me dokar ta ƙunsa?

Shugaban ƙaramar hukumar Ranon, ya shaida cewa lalacewar tarbiyya ce dalilin bijiro da wannan doka, don haka ya zame musu dole domin tabbatar da kyakkyawan tarbiyya tsakanin matasa da zawarawa a wannan zamanin.

Ya ce daga yanzu iyaye da sauran al’ummar gari za su tabbatar ana zance bisa tsari na zamantakewa da al’adu da addini Musulunci.

“Mun umarci shugabanni da limamai da sauran masu Ruwa da tsaki a Cikin al’umma su kasance masu sanya ido a kan yadda ake zance a wannan kasa ta mu, jami’an Hisba da ‘yan sanda da sarakuna za su tabbatar da ganin ana bin wannan umarni.” Hon. Ruwan kanya

Sannan ya kara da cewa jami’ai za su rika sintiri domin tabbatar da cewa kowa ya bi wannan umarni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...