Zamu rika share lungu da sakon Hukumar RUWASA kullum – Kwamred Salisu Bichi

Date:

BY SANI MAGAJI GARKO

Shugaban hukumar samar da ruwansha Mai tsafta a yankunan karkara ta jihar Kano RUWASA Kwamred Ibrahim Salisu Bichi ya ce yanzu kullum zasu rika share kowanne loko da sako na hukumar a kullum.

Kadaura24 ta rawaito Ibrahim Salisu Bichi ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa Wanda hakan ke a matsayin martani kan waadin kwanaki uku da maaikatar Muhalli ta jihar Kano ta bawa hukumar domin tsaftace muhallansu biyo bayan gazawarsu na tsaftace hukumar a lokacin tsaftar Muhallin ta Kasuwanni da maaikatu harma da hukumomin Gwamnati da aka gudanar a 27 ga watan Ogustan 2021 da ya gabata.

Idan zaa iya tunawa a juma’ar da ta gabata ne maaikatar Muhalli ta bayyana takaicinta sakamakon samun hukumar RUWASA cikin datti da tara shara baa debe ba da kuma gaza samun wani daga cikin shugabannin maaikatar da zai tarbi kwamitin koli na tsaftar Muhallin na jihar Kano.

To amma Kwamared Ibrahim Salisu Bichi ya ce ko yanzu aka saka gasar tsafta a maaikatu da hukumomin Gwamnatin Kano RUWASA ce za tayi na daya.

Shugaban na RUWASA daga nan ya roki maaikatar Muhalli ta jihar Kano da ta samar wa da hukumar bokitin Tara shara, yana mai cewa matsalar da aka samu yanzu tana da alaka da matsala bokiti da Babu yanzu a hukumar.

“An aiko mana da takardar ziyara, maaikatanmu suna ta kokari duk sun tara shara domin jihar Kano ta ce tana so yanzu shara ta zama kudi, to munyi sharar mun tara ta muna jiran azo a kwashe ne sai kuma Allah ya kawo kwamishinan Muhalli ya ga inda aka tara sharar.

RUWASA Ma’aikata ce ta da take tara mutane da yawa (sama da 50 a kullum) musamman daga yankunan karkara, wani zai shara ruwan leda ya saki ledar bamu gani ba tunda sai mun tashi zamu duba domin tsaftace loko da sako da wannan maaikata”.inji Bichi

Kwamared Salisu Bichi ya bada da tabbacin cewa matsala da aka samu tuni ta zama tarihi domin tuni an magance ta.

134 COMMENTS

  1. Джошуа – Усик. Прогнозы и ставки букмекеров Энтони Джошуа (24-1, 22 КО) — фаворит букмекеров перед боем с Александром Усиком (18-0, 13 КО) за три чемпионских пояса в супертяжелом весе. Энтони Джошуа Александр Усик смотреть онлайн Усик не стал. И не станет. Ему роль такую прописали – помогать нести яйца. Джошуа несёт яйца. И в данном бою он должен снести яйцо с помощью Усика. А потом повтороно – ещё одно яйцо. Ну, принято

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...