Ya kamata a Rika yiwa Saurayi da Budurwa gwajin Kwayoyi kafin Aure – Shugaban NDLEA

Date:

Daga Zainab Muhd Darmanawa

Shugaban Hukumar Yaki da ta’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA, Rtd. Janar Muhammad Buba Marwa ya bayar da shawarar a Rika yinn
gwajin miyagun kwayoyi kafin aure ga saurayi da budurwa.

Kadaura24 ta rawaito Buba Marwa ya ce gwajin zai taimaka matuka wajen yaki da shaye -shayen miyagun kwayoyi da amfani da miyagun kwayoyi a kasar nan.

Shugaban na NDLEA ya bayyana hakan a Kano lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Buba Marwa ya bayyana cewa Hukumar ta samar da hanyoyin da za su rage barazanar shan miyagun kwayoyi a cikin kasar nan.

Shugaban na NDLEA ya ce Hukumar ta kwace miyagun kwayoyi Kilogram miliyan 2 daga watan Janairu lokacin da ya shiga ofis zuwa yau. Magungunan sun kai sama da Naira miliyan ɗari ,Yayin da yace sun Kama Mutane sama da Dubu takwas Masu saafara da tu’ammali da Miyagun kwayoyi

Shugaban na NDLEA ya kuma an kama mutane 8000 kuma an gurfanar da 1 600 a gidan yari tun bayan Zaman sa Shugaban Hukumar NDLEA.

A nasa jawabin, Gwamna Abdullahi Ganduje ya nuna farin Cikin bisa ziyarar tasa tare da yin alkawarin jajircewar gwamnatinsa na rage barazanar shan miyagun kwayoyi a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An sanya dokar hana fita a Jigawa

An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare...

Gwamnan Kano ya bayyana abun da gwamnatin za ta yi a filin Idi

  Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar...

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...