Mutanen gari sun kama ’yan bindiga a Zariya

Date:


Mutanen gari sun yi kukan kura sun cafke masu garkuwa da mutane da suka kai hari a unguwar Low Cost da ke Zariya.

A halin yanzu, wasu daga cikin ’yan bindigar suna hannun ’yan sanda bayan da mutanen unguwar suka yi musu kofar rago ranar Lahadi da tsakar dare.


Duk da haka, masu garkuwar sun tafi da matan aure biyu daga gidaje daban-daban, amma sun sako kananan yara biyun da suka dauka da tare da daya daga cikin matan, sai dai ba su sako mahaifiyar yaran ba.

Majiyarmu a Zariya ta ce ’yan bindigar sun harbi kananan yara almajirai guda hudu a lokacin farmakin da suka kai.

Daily Trust ta gana da almajiran da raunukan harin a jikinsu, kuma a halin yanzu suna samun kulawa a asibitin New City da ke a Zariyan.

74 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...